Her Excellency Hajiya Hauwa Raɗɗa ayayinda takeba Maniyyata aikin Hajji Abinci da ruwa da Hannayenta. Jirgi na 4

An yi kira ga Alhazan Jihar Katsina da su yi ma Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Mal. Dikko Umar Radda da Mahaifiyar shi, da Jihar Katsina Addu’a, haka Kuma su yi Kasa da Arewacin Najeria, Musamman Jahohin Zamfara, Sokoto, Kogi Da Maiduguri Addu’o’i,

Haj. Hauwa Umar Radda Uwargidan Tsohon Shugaban Kasar Nigeria Kuma Yaya ga Maigirma Gwamnan Jihar Katsina itace ta yi wannan kira a daidai lokacin da take raba ma Alhazan Jihar Katsina Jirgi na 4, Abincin Rana da Ruwan sha, a Karkashin Kungiyar ta ta HAUWA RADDA MU’ASSATUL KHAIRIYYA, a Ranar Alhamis 22/05/2025.

Haka zalika Haj. Hauwa Umar Radda tayi kira ga masu Hannu da Shuni da su yi koyi da wannan Kungiya, a cewar ta itama tayi koyi da Wata Kungiya da ta gani a Kasar Saudiyya, ta Kuma yi ma Alhazan Fatan Alkhairi da Addu’ar yin Ibada Karbabiya.

 

Alhazan da suka amfana da Tallafin Sun yi Mata Fatan Alkhairi da Addu’a Gamawa lfy.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More Articles & Posts