Dr.Hajiya Hauwa Radda Ta Kaddamar Da Raba Tallafin Kayan Sana’oi Ga Mata Masu Kananan Sana’oi

 

Dr.Hajiya Hauwa Radda Ta Kaddamar Da Raba Tallafin Kayan Sana’oi Ga Mata Masu Kananan Sana’oi

Shugabar Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Mu’assasatul Khairiyya Dr.Hajiya Hauwa Radda, ta raba tallafin kayan sana’oi ga mata masu kanana sana’oi a Jihar Katsina.

Dr.Hajiya Hauwa Radda ta raba ta kaddamar da raba tallafin ne ga wasu mata masu kananan sana’oi da aka zabo daga bangarori daban-daban na Jihar Katsina.

Wadanda suka amfana da tallafin sun hada da mata masu kiwon kaji da masu kuli-kuli da awara da masu saida fura gami da masu sana’ar dinkin hula.

Da take mika tallafin, Shugabar Gidauniyar Mu’assasatul Khairiyya Dr.Hajiya Hauwa Radda ta bayyana cewa, wadanda suka amfana din za’a baiwa wasu daga cikin su tallafin kudi, domin sayen kayan aiki.

Dr.Hajiya Hauwa Radda ta bayyana cewa, kayayyakin Gwamna Radda ne ya samar da su, domin rabawa ga mata masu kananan sana’oi a fadin Jihar Katsina.

Ta tabbatar da cewa, za’a cigaba da raba kayan ga mata da aka zabo a Kananan Hukumomin domin su amfana.

Daga nan sai ta yi kira ga matan da suka amfana akan su sakawa karamcin ta hanyar yin addu’ar nasara ga Gwamna Dikko Umaru Radda.

A nata jawabin, Babbar Jami’ar Gidauniyar Mu’assasatul Khairiyya a Shiyyar Katsina Hajiya Hashiya Sani Bindawa, ta magantu akan dumbin ayyukan tallafawa al’umma da Dr.Hajiya Hauwa Radda ke gudanarwa.

Wasu daga cikin matan da suka amfana da tallafin, sun jinjinawa Dr.Hajiya Hauwa Radda da Gwamna Dikko Radda akan tallafa masu da kayan sana’oin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More Articles & Posts