
Dr.Hajiya Hauwa Radda Ta Zama Uwar Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Zango
….. Ta Karbi Bakuncin Limaman Juma’a Na JIBWIS Daga Wasu Kananan Hukumomi
Wadda ta assasa gidauniyar tallafawa al’umma ta Mu’assasatul Khairiyya Dr.Hajiya Hauwa Radda, ta zama uwar Hukumar Hisbah reshen Karamar Hukumar Zango.
An mika takardar nadin nata ne a matsayin uwar Hukumar a lokacin da ta karbi bakuncin wasu limaman juma’a na Kungiyar JIBWIS daga wasu Kananan Hukumomi.
Ziyarar dai na da nufin yin dubiya ga Dr.Hajiya Hauwa Radda, bayan ta dawo daga ziyarar neman lafiya a kwanan nan.
Da yake magantawa a lokacin ziyarar, Malam Ashiru Mai’adua wanda ya yi jawabi a madadin limaman ya ce, ziyarar tasu na a matsayin bagire na yin jaje ga Dr.Hajiya Hauwa Radda bayan dawowa daga ziyarar neman lafiya.
Malam Ashiru Mai’adua ya magantu akan yadda take bakin kokarin ta wurin tallafawa cigaban addinin Islama da taimakon marayu da masu karamin karfi.
Ya yi addu’a akan Allah SWT ya kara yi mata jagoranci ta fuskar gudanar da wadannan ayyuka.
Tunda farko, babban jigo na Gidauniyar ta Mu’assasatul Khairiyya Alhaji Ali Talakka, ya yabawa Hukumar ta Hisbah ta Zango akan nadin da suka yi wa Hajiya Hauwa Radda.
Alhaji Ali Talakka ya yi magana mai tsawo akan ayyukan jin kan al’umma da gidauniyar ke aiwatarwa a fadin Kananan Hukumomi 34 na Jihar Katsina.
Da take maida jawabi, Dr.Hajiya Hauwa Radda ta nuna farin cikin akan kulawar da limaman suka yi akan ta, sai ta sha alwashin cigaba da yin bakin kokarin ta wurin tallafawa cigaban addinin Islama.
Ta kuma nuna farin ciki akan nadin da Hisbah ta Zango ta yi mata a matsayin uwar Hukumar, tare da bada tabbacin cigaba da tallafawa ayyukan Hukumar, domin kawo cigaba da gyaran tarbiyya a cikin al’umma.
Daga bisani Dr.Hajiya Hauwa Radda ta mika makullan mota kirar Passat ga Kwamandan Hisbah na yankin, wadda Shugaban Karamar Hukumar Zango ya siya ga Hukumar Hisbah reshen garin Yardaje da ke Karamar Hukumar.







Leave a Reply