
Hajiya Hauwa Radda, Shugabar Kungiyar Hauwa Radda Muassatul Khairiyya, Yaya ga Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Mal Dikko Umar Radda PhD ta amshi bakuncin Wakillan Gidan Baban Limamin Masallachin Juma’a na Kofar Soro.
Makasudin Ziyarar shine don sada Zumunchi tare da Gudanar da Addu’o’i ga Maigirma Gwamna da Hajiya Hauwa Radda, tare da Jihar Katsina.
Jagoran tafiyar Malam Muttaqa Imam, shine ya Jagorancin yin Addu’o’in, tare da kara nuna goyon bayan su ga Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda, musamman irin yadda ya Kula da Talakkan Jihar Katsina.
A nata Jawabin Shugabar Kungiyar Hauwa Radda Muassatul Khairiyya, ta yi Godiya musamman yadda suke sa Dan’uwan ta a cikin Addu’o’in su a kodayaushe, Kuma ta kara da cewa a Shirye suke da ci gaba da taimakon Addinin Musulunci da Al’ummar Jihar Katsina. Ta Kuma yi masu Addu’ar komawa Gida lfy






Leave a Reply