0
Sama da Alhazan Jihar Katsina 500 Jirgin Farko na shekarar 2025, suka amfana da Tallafin Abinci da Ruwa na dare, Daga Uwar Kungiyar MU’ASSATUL KHAIRIYYA, Haj. Hauwa Umar Radda.
Da yake Jawabi Amadadin ta Alh. Aliyu Talakka yace ciyarwar an saba yin ta duk shekara, ya Kuma kara da cewa zaa ci gaba da kawo ma Alhazan Abinci da Ruwa sau Biyu a Rana har sai an gama kwashe Alhazan.
Alhazan Sun nuna Farincikin su da Godiya tare da Addu’o’i ga Haje. Hauwa Umar Radda da Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Mal Dikko Umar Radda.
Leave a Reply